An hallaka sojojin Najeriya a harin kwantan-bauna a jihar Neja

0
175

Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta ce wasu ƴan bindiga sun kashe sojojinta shida a wani harin kwanton-ɓauna da suka kai musu a Jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Lahadi da maraice, ya ƙara da cewa su ma sojojin Nijeriya sun kashe ƴan bindiga da dama yayin fafatawar.

A cewarsa, ƴan ta’addan sun yi kwanton-ɓauna ga dakarunsu da aka tura wasu yankunan ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja ranar 19 ga watan Afrilun 2024, inda suka gwabza faɗa “sannan suka kawar da ƴan ta’adda da dama tare da karɓe wasu daga cikin makamansu”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here