Dan Najeriya ya kafa tarihin bajinta a wasan dara na chess

0
141
Tunde Onakoya

Wani gwarzon ɗan wasan dara, dan Najeriya kuma mai kishin ilimin yara ya buga wasan chess na tsawon awa 58 ba tsayawa a dandalin Times Square na birnin New York City.

Hakan yunƙuri ne na kafa sabon tarihi a kundin bajinta na Guinness World Record ajin wanda ya fi daɗewa yana buga wasan chess ba dakatawa.

Tunde Onakoya, ɗan shekara 29, yana fatan tara dala miliyan ɗaya don ilimin yara a faɗin Afirka, ta hanyar yunƙurin kafa tarihin bajinta da ya fara ranar Laraba.

A daidai ƙarfe 2 da rabi na safiyar Asabar ne Tunde ya haura awanni 58, inda hakan ke nufin ya haura tarihin da ake da shi a yanzu na buga chess ba tsayawa, na awa 56, da minti 9 da sakan 37, wanda a 2018 Hallvard Haug Flatebø da Sjur Ferkingstad daga Norway suka kafa.

Zuwa yanzu, hukumar kundin bajinta ta Guinness World Record ba ta fitar da sanarwa ba game da yunƙurin na Tunde. A wasu lokutan yakan ɗauki ƙungiyar makonni kafin ta tabbatar da sabon tarihin bajinta.

Gagarumin goyon baya

Tunde Onakoya ya kara da Shawn Martinez, zakaran wasan chess na Amurka, kamar yadda ƙa’idojin hukumar Guinness World Record suka tanada cewa wajibi ne duk wani yunƙurin kafa tarihi ya haɗa ‘yan wasa biyu da za su buga wasa ba tsayawa har na tsawon lokacin.

Tunde na ta samun ƙaruwar magoya baya a intanet da ma dandalin da yake wasan, inda aka ji kiɗan Afirka na tashi don nishaɗantar da ‘yan kallo da magoya baya da suke tafi suna jinjina masa.

Yunƙurin kafa sabon tarihin bajintar don “tabbatar da burin miliyoyin yara ne a faɗin Afirka waɗanda ba sa iya zuwa makaranta,” cewar Tunde Onakoya, wanda shi ne ya kafa ƙungiyar sa-kai ta Chess in Slums Africa a shekarar 2018.

Ƙungiyar tana da burin tallafa wa ilimin aƙalla yara miliyan 1 a unguwannin marasa galihu a nahiyar Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here