Tinubu na sane ya bai wa ‘yan arewa manyan mukamai – Nuhu Ribadu

0
187
Ribadu

Mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, a ranar Alhamis ya ce Shugaba Tinubu yana sane ya naɗa ‘yan arewa manyan muƙamai.

Ribaɗu ya bayyana haka ne a Sokoto yana cewa shugaba Tinubu ya ɗauki ‘yan arewa ya sa a wasu mukamai masu muhimmanci saboda yana son a kawo karshen rikicin yankin.

Da yake gabatar da wata maƙala kan “shawo kan matsalolin tsaro da arewa ke fuskanta a Najeriya” wanda wani bangre ne na yaye ɗaliban aji na 38, 39, 40 da kuma 41 na Jami’ar Danfodiyo da ke Sokoto, ya nuna bacin rai kan matsalolin da arewa ke fuskanta kama daga matsalar tsaro zuwa yaran da ba sa zuwa makaranta da dai sauransu.

Ya kuma ƙara da cewa talaucin da yankin ke ciki na ƙara ta’azzara a kullum.

“Yayin da Tinubu yake kada gwamnatinsa, ya sanya Arewa a tsakiyar zuciyarsa kuma yana shirin yin komai domin ceto yankin daga halin da yake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here