‘Yan takarar shugabancin kasa za su sanya hannu kan zaman lafiya

0
135

Kwamatin zaman lafiya na kasa ya gayyaci jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar shugaban kasa da masu magana da yawunsu domin sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya.

Za a gudanar da taron sanya hannun ne a ranar 29 ga watan Satumbar da muke ciki a Abuja.

Shugaban kwamatin kana tsohon shugaban kasar nan Abdulsalami Abubakar ya ce za a sanya hannun ne har sau biyu a gabanin zaben 2023.

Ya ce manufar sanya hannun akan yarjejeniyar zaman lafiyan shi ne dabbaka zaman musamman lokutan yakin neman zabe.