Isra’ila za ta ɗauki matakin da ya dace kan Iran – Netanyahu

0
168

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya faɗa wa Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya David Cameron cewa ƙasarsa “za ta ɗauki mataki da kanta” kan harin da Iran ta kai mata. 

Ya ce gwamnatinsa za ta yi “duk mai yiwuwa wajen kare kan ta” yayin ganawar da gwamnatin Birtaniya ke fatan za sa Isra’ila ta sassauta kan batun harin. 

Mista Netanyahu ya jaddada cewa za su rama harin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ta kai mata ranar Asabar. 

Mista Cameron ya faɗa masa cewa duk martanin da za su mayar ya kamata ya zama “cikin nutsuwa” kuma maras girma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here