Ba’a kyauta mana mu talakawa – Rukayya Dawayya

0
123

Jarumar Kannywood, Rukayya Dawayya ta shawarci ‘ya’yan talakawa da su farka daga baccin da suke yi domin ‘ya’yan masu kudin da ke soyayya da su ba aurensu za su yi ba.

Dawayya ta ce sam masu kudi basa yiwa talakawa adalci domin basa yarda ‘ya’yansu su auri kowa sai ‘ya’yan masu kudi yan uwansu.

A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, jarumar ta kalubalanci ‘ya’yan talakawa da su tashi su nemi ilimi don kare mutuncin kansu a kasar nan.

Shahararriyar jarumar Kannywood, Rukayya Umar Dawayya ta yi martani a kan yadda ake yin kwarya tabi kwarya wajen kulla auratayya a kasar nan.

Dawayya ta shawarci ‘ya’yan talakawa da ke da kyau a kan su daina yarda da soyayya tsakaninsu da yaran masu kudi domin magana ta gaskiya ba auransu za su yi ba.