Mun yi fata-fata da sansanonin ‘yan ta’adda guda 3 a Zamfara – Sojoji

0
206

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta yi luguden wuta kan wasu sansanonin ‘yan ta’adda guda uku a jihar Zamfara ranar Laraba, inda ta ce ta kashe ‘yan ta’addar masu dama bayan lalata wuraren nasu.

Mai magana da yawun rundunar, AVM Edward Gabkwet wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis din nan, ya ce an cimma nasarar ne sakamakon ayyukan wani farmaki daya daga cikin ayyukan da rundunar Hadarin Daji ke yi a yankin.

Gabkwet ya kara da cewa sansanonin da aka lalata na dan ta’adda Abdullahi Nasanda ne da ke Zurmi da Malam Tukur da ke Gusau da kuma a karamar hukumar Maradun duka a jihar ta Zamfara.

“Bayan tabbatar da cewa ayyukan da suke yi na ta’addanci ne sai jirage suka rinka an taya bama-bamai inda kuma aka kashe ‘yan ta’addar masu dama.” In ji Gabkwet.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here