Rundunar ‘yan sanda ta haramta hawan dawaki a Minna yayin bikin Sallah

0
161
Hawan Sallah

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta haramta hawan dawaki a babban birnin jihar Minna yayin bukukuwan karamar Sallah da ke tafe a mako nan, a wani yunkuri na kange hadarin da ake fuskanta a duk irin wannan lokaci.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, Shawulu Ebenezer danmamman da ke bayyana wannan mataki a sakon sallar da ya aikewa jama’a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Wasiu Abiodun ta ce wannan mataki na da nufin kawo karshen yadda a kowacce shekara ‘yan daba kan yi amfani da hawan dawakin wajen farmakar jama’a.

A jihar Neja kusan duk shekara akan samu hare-haren ‘yan daba a lokacin bukukuwan sallah wadanda ke fakewa da hawan dawakin da jama’a ke yi.

A cewar sanarwar yanzu haka an rarraba jami’ai dubu 2 da 500 a sassan jihar don bayar da kariya a filayen sallar idi da ke kananan hukumomin jihar 25 baya ga wuraren shakatawa da sauran wajen taruwar jama’a.

Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago ya bukaci al’ummar jihar ta Neja mai fama da hare-haren ‘yan bindigar daji da suyi amfani da damar bikin sallar wajen addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a sassan jihar dama sauran jihohin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here