Shettima ya isa Borno don gudanar da bikin sallah

0
175

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya isa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno domin gudanar da bikin sallah karama.

Shettima ya isa filin jirgin samanna Muhammadu Buhari da ke Maiduguri, inda ya samu tarba daga mataimakin gwamnan Borno, Alhaji Umar Kadafur, da ‘yan majalisar zartarwa na jihar da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar.

A halin da ake ciki dai an tsaurara matakan tsaro a Maiduguri da kewaye kamar yadda aka saba a lokutan bukukuwa sallah.

Ana sa ran gudanar da bikin sallah ne a ranar Talata ko Laraba, ya danganta da ranar da aka watan Musulunci na Shawwal.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here