Gwamnatin Zamfara ta musanta ciyo bashin naira biliyan 14.26

0
166

Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa ba ta ciyo rancen kuɗi naira biliyan 14.26 ba, sai dai kuɗin wani ɓangare ne na kuɗaɗen da gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo na naira biliyan 20.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar ta Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce gwamnati ba ta ci wani bashi a gida ko waje ba tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal.

“Muna so mu fayyace rahoton ofishin kula da basussuka (DMO) cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ciyo bashin Naira biliyan 14.26.

“Gwamnatin jihar Zamfara ba ta taɓa neman buƙatar karɓar rance ba ko tuntuɓar majalisar jiha ko ta ƙasa domin neman wannan buƙata,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce ya kamata jama’a su gane cewa gwamnatin baya ce a jihar ta ciyo bashin kuɗin na naira biliyan 20, amma ta ƙasa karɓar kuɗaɗen duka.

“Gwamnatin da ta gabata ta karbi naira biliyan 4 daga cikin rancen biliyan 20 da aka nema domin aikin filin jirgin sama na Zamfara, duk da cewa ba a yi amfani da kuɗaɗen ba.

“Bayan da muka shigo ofis, mun gano cewa sharuɗan biyan kuɗin ya sa kawo karshen yarjejeniyar ba zai yiwu ba ba tare da ya jawo babbar asara ga jiha ba,” in ji sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here