Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai a jihar Delta

0
172

Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da ba a san adadinsu ba da ke tafiya a kan hanyar East-West a Ugheli, jihar Delta.

Direban motar ya ranta a na kare ba tare da samun ko rauni ba. Kakakin Rundunar ƴan sandan Jihar Delta Edafe Bright ya bayyana cewa wataƙila fasinjojin cikin motar ɗalibai ne da ke dawowa daga makarantarsu a Calabar, Jihar Cross River ranar Juma’a da daddare, kafin a yi garkuwar da su a karamar motar bas da suke ciki.

Ya ce ya zuwa yanzu ba a buƙaci a biya kuɗin fansa ba. Sai dai kuma, ƴan sanda sun bazama neman mutanen da suka yi garkuwa da ɗaliban.

“Hedkwatar ƴan sanda na sane da wannan mummunan al’amari, kuma muna yin duk mai yiwuwa don tabbatar da an kuɓutar da su ba tare da wata matsala ba,” in ji Bright a saƙon da ya wallafa a shafin X.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun sace ɗaliban jami’a da dama a jihar Cross River mai maƙwabtaka.

A Nijeriya, ƴan bindiga na yawan garkuwa da ɗalibai a makarantunsu tare da neman kuɗaɗen fansa kafin su sako su, lamarin da ke kara ta’azzara sha’anin tsaro a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here