Sojoji sun tarwatsa sansanin IPOB a Imo

0
165

Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro sun tartwatsa sansanin ƴan ƙungiyar IPOB da takwararta ta ESN da ke cikin dajin Ezioha a karamar hukumar Mbaitoli na jihar Imo.

Sojojin sun kai samame sansanin ne a ranar Alhamis, a wani yunkuri na kakkaɓe ƴan IPOB ɗin da kuma ƙawayesnu na ESN da ke iyaka da kogin Njaba da ke makwabtaka da al’ummar Awo-Omama a jihar ta Imo.

Yayin samamen, sojojin sun yi artabu da ɓata-garin, inda hakan ta sa suka tilasata wa wasu daga cikinsu tserewa zuwa cikin dazuka tare da munanan raunuka.

Sanarwa da sojojin suka fitar a shafin X, ta ce sun samu nasarar tono wasu abubuwan fashewa da aka binne da nufin hana sojoji kai wa wajen da ƴan IPOB ɗin suke.

Haka kuma, sun tono wasu gawawwakin wasu mutane da aka kashe bayan garkuwa da su, waɗanda aka binne a wasu ramuka a sansanin.

Sojojin sun ce za a je a gudanar da bincike kan gawawwakin kafin sake yi musu bizina ta ban-girma.

Cikin kayayyakin da suka kwato sun haɗa da babur guda ɗaya, abubuwan fashewa uku, akwatin rediyo bakwai, sarkuna, katin cirar kuɗi na ƙasar waje, layukan waya biyu, katunan zaɓe biyu da kuma lambar mota.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here