Munich ba za ta lashe Bundesliga ba – Tuchel

0
284

Kocin Bayern Munich Thomas Tuchel ya ce gasar ɗaukar Bundesliga ta ƙare bayan rashin nasarar da ya yi da ci biyu babu ko daya a hannun Borussia Dortmund, duk da cewa a kwai wasa bakwai da ya yi ragowa a kakar.

Kwallayen da Dortmund ta ci sun fito ta hannun Karim Adeyemi da Julian Ryerson, nasarar farko da ta samu kan Munich a wasan hamayya na Der Klassiker tun 2019.

Da wannan rashin nasara, yanzu maki 13 ne tsakanin Leverkusen da ke ta ɗaya da Bayern da ke matsai na biyu.

Ko da aka tambaye shi ko Bayern ta hakura da wannan kofin, sai Tuchel ya ce “eh ko shakka babu.”

A makon jiya ne kocin Leverkusen Xavi Alonso ya bayar da tabbacin ci gaba da zama a ƙungiyar, wanda hakan ya kawo ƙarshen jita-jitan da ake yi na maye Jurgen Klopp a tsahuwar kungiyarsa Liverpool.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here