WHO ta yi gargadin majinyata 9,000 a Gaza ne ke bukatar taimakon gaggawa

0
157
Asibitin Gaza

Shugaban Hukumar lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce majinyata dubu tara ne a Gaza ke bukatar a dauke su daga yankin zuwa wani wuri don samun taimakon da ya dace, sakamakon yaki da ya lalata asibitocin yankin, inda yanzu da wuya a samu asibitoci 10 dake aiki a Gazan.

A wata kididdiga da WHO ta fitar a baya kafin a fara yakin Isra’ila da Falasdinu akwai akalla asibitoci 36 dake aiki a yankin, yayin da a yanzu da wuya a samu 10 daga ciki da ke aiki.

Ghebreyesus ya ce a cikin marasa lafiya dubu taran da ya kamata a gaggauta ficewa da su daga Gaza, akwai masu fama da cutar daji, da koda, da wadanda buraguzan gini suka ruguzo musu da ma sauran da ke fama da matsanancin raunuka sakamakon yakin.

Isra’ilar dai ta sha alwashin gama wa da Gaza kwatata bayan da kungiyar Hamas ta kai mata harin da yayi sanadiyar mutuwar Yahudawa da yawa a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here