An kama mutum takwas kan zargin kashe yan sanda a Delta

0
158
Yan sanda
Yan sanda

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da kama mutum takwas waɗanda ake zargi da hannu a kashe jami’anta shida a dajin Ohoro da ke Ƙaramar Hukumar Ughelli North a Jihar Delta.

Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar inda ya ce a halin yanzu waɗanda ake zargin suna hannu kuma ana gudanar da bincike a kansu.

Ya bayyana cewa sun yi nasarar kama mutanen da ake zargin bayan gudanar da bincike mai zurfi, inda ya ce tun can dama an kama mutum biyar jim kaɗan bayan kashe jami’an ƴan sandan, sai kuma sauran ukun aka kama su a wurare daban-daban.

An kashe ƴan sandan ne a wani harin kwanton-ɓauna da aka kai musu a lokacin da suke hanyar zuwa aikin ceto.

Ƴan sandan da aka kashe sun haɗa da Inspector Abe Olubunmi da Inspector Friday Irorere da Sergeant Kuden Elisha da Sergeant Akpan Aniette da Sergeant Ayere Paul da kuma Sergeant Ejemito Friday.

Rundunar ƴan sandan ta kuma jaddada cewa za ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin ganin an hukunta duka waɗanda suke da hannu a kashe jami’an nata.

Jihar Delta ta fuskanci rikice-rikice a baya-bayan nan musamman kan batun kashe jami’an tsaro inda ko a ranar 14 ga watan Maris ɗin nan sai da aka kashe sojojin Najeriya 17 a jihar.

Wannan lamarin ya tayar da hankalin jama’ar ƙasar inda a nasu ɓangaren su ma sojojin ƙasar suka lashi takobin zaƙulo waɗanda suka kashe jami’an nasu tare da hukunta su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here