Kisan Delta: Basaraken da sojoji ke nema ya mika kan sa

0
219

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Rivers ta miƙa Sarkin Ewu Clement Ikolo Oghenerukevwe ga sojoji bayan rundunar ta ayyana shi a matsayin wanda take nema bisa zargin sa da hannu a kisan sojoji.

Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ce a jiya Alhamis ne basaraken ya miƙa kan sa ga ofishin ‘yan sandan bayan wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar inda a ciki ta bayyana mutum takwas da take nema ruwa a jallo bisa zargin hannunsu a kisan dakarunta 17 a yankin Ughelli na jihar.

Cikin mutanen da take neman har da Farfesa Ekpekpo Arthur, da mahaifiyar ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi da kai harin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a safiyar yau Juma’a ne aka miƙa shi ga sojojin, kamar yadda kakakin rundunar ya shaida mata.

Sai dai basaraken ya musanta zargin da sojojin suke yi masa yayin wani taron manema labarai kafin daga baya ya miƙa kan nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here