Rundunar sojin Najeriya na neman mutum 8 ruwa-a-jallo kan kisan dakarunta a Delta

0
160
Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta fitar da hotunan wasu mutane da take nema ruwa-a-jallo bisa zargin kisan dakarunta goma sha bakwai a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, kwana guda bayan an yi wa sojojin jana’izar ban-girma a Abuja, babban birnin ƙasar.

Mutanen takwas, ciki har da mace, su ne Akevwru Daniel Omotegbono wanda aka fi sani da suna Amagbem; Prof. Ekpekpo Arthur, Andaowei Dennis Bakriri da Igoli Ebi.

Sauran su ne Akata Malawa David, Sinclair Oliki, Clement Ikolo Oghenerukevwe da kuma Reuben Baru.

Kusan mako biyu kenan Shugaba Tinubu ya bai wa hedkwatar tsaro da shugaban rundunar tsaron Najeriya “cikakken iko” na hukunta duk wanda aka samu da laifin kisan sojojin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here