Gwamnatin tarayya ta ayyana hutu ranar juma’a da litinin masu zuwa

0
191
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma’a, 29 ga watan Maris da Litinin, 1 ga watan Afrilu a matsayin hutu albarkacin bukukuwan Easter da Kiristoci za su yi a faɗin Najeriya.

Ministan Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba.

Ya buƙaci mabiya addinin na Kirista da su yi amfani da lokacin wajen kwaikwayon halayen sadaukarwa, kaunar juna, yafiya, soyayya, hakuri da zaman lafiya da Annabi Isah (A.S) ya koyar

Cikin sanarwar da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Cikin Gida, Dokta Aishetu Gogo Ndayako ta fitar, ta ambato ministan yana kira ga ’yan Nijeriya da su yi amfani da lokacin wajen yaɗa soyayya da ƙaunar juna da kuma tausayawa wajen tabbatar da haɗin kai da samun aminci.

Ministan ya buƙaci mabiya addinin Kirista da su yi amfani da waɗannan kyawawan dabi’u domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar ƙasar.

Kazalika, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su yi himmatu wajen bayar da sadaka da kyautar kayayyaki buƙata musamman a tsakanin jama’ar da ke da rauni.

Ministan ya kuma buƙaci ’yan Nijeriya da su ci gaba da bai wa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed goyon baya a ƙoƙarin da take yi na tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here