NDLEA ta ja hankalin mutane kan sabuwar hanyar da ake ha’intar matafiya da ita

0
220

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ja hankalin al’umma musamman matafiya zuwa ƙasashen waje kan sabuwar hanyar zambar da ake yi da sunan jami’an hukumarsu.

Kakakin hukumar Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a ranar Asabar a Abuja, yana cewa masu zambar suna kira iyalan matafiya suna kiran ‘yan uwansu suce sun kama su a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas ko kuma wani filin jirgin su ce an kama su da kwayoyi yayin saukarsu.

“Bayan jefa iyalan cikin firgici sai masu zambar su sake kiran ‘yan uwan mutanen su nemi a biya su miliyoyin nairori domin ganin yadda za a yi a saki wanda aka kama da yanzu ake tsare da shi a hannun NDLEA,” in ji Femi.

“Mun daƙile irin wadannan laifuka a bya, wani lokacin iyalan ke kiran jami’anmu domin neman tabbaci kan lamarin.”

Sannan kuma ya musanta hannun jami’ansu cikin abin da ya faru a bayan nan, inda aka ji muryar wani mutum da ya ce shi jami’in NDLEA ne yana tattauna yadda wata mata za ta biya naira miliyan biyar domin sakin wani mutum da ya zo daga Amurka da ya ce sun kama shi a filin jirgin MMIA da ke Legas a ranar 22 ga watan Maris, kuma an same shi da kwayoyi.

Daga baya aka shawarce su ka da su biya kuɗin da aka nema.

Femi ya shawarci al’umma su kiyayi tattaunawa da iyalansu kan tafiyar da ke gabansu, somin kaucewa irin wannan zambar da maha’intar ne ke shiryawa.

Ya kuma bayar da lambar wayar hukumarsu ga duk mutumin da ya samu kansa a irin wannan yanayi ya yi maza ya shaida musu +2347064670026 and +2348033326327.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here