Gwamnatin Kano ta ci gaba da rusau duk da umarnin kotu

0
228
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Wasu mutane sun koka kan yadda hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), ta rushe musu gine-gine sama da 30 a yankin garin Gurungawa da ke Karamar Hukumar Kumbotso.

Daily trust ta ruwaito yadda wata babbar kotu a jihar karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Ibrahim Mahmoud, ta dakatar da KNUPDA daga rushe duk wani gini da ke yankin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙarar da ke gabanta.

Sai dai duk da wannan umarni, hukumar ta rushe wasu gine-gine a unguwar a ranar Juma’a, 15 ga watan Maris, 2024.

Da yake karin bayani kan lamarin, lauyan wadanda suke kara, Abubakar Alhaji Rabi’u Doka wanda ke wakiltar mutum 23, ya ce sun yi mamakin matakin da KNUPDA ta ɗauka.

“Wadanda nake karewa sun samu umarni daga babbar kotun jiha a ranar 22 ga watan Disamba, 2023, inda Mai Shari’a Aisha Ibrahim Mahmoud ta dakatar da KNUPDA daga rushe kowanne gini har sai an kammala shari’a.

“Amma abin ya ba mu mamaki, yadda KNUPDA ta yi watsi da umarnin kotu, inda ta ci gaba da rushe gine-ginen mutane.

“Za mu shigar da sabuwar kara. Hujjarmu ita ce KNUPDA ta ki bin umarnin kotu, wanda hakan ya janyowa masu kadarorin asarar dukiya.

“Masu shigar da kara sun mallaki fili kusan 32, kuma za su nemi diyyar asarar da aka yi musu ta hanyar doka.”

Ita ma KNUPDA ta bakin lauyanta, Barista Salisu M. Tahir ta ce, “Mun samu korafe-korafe daga wasu da suka yi ikirarin mallakar wurin kuma mun ba su takardar izinin tashi amma shiru babu amsa.

“Bayan mun sanya alamar rusau a wurin ne sai suka aiko da amsa kuma suka gaza ba mu takardar shaidar yin ginin wanda hakan ya ci karo da sashe na 12, 13 da 14. Mun nemi su tsaya amma suka ki.

“Kazalika, mun samu takardun da ke nuna shaidar mallakar wajen, amma da muka yi bincike sai muka gano cewa tasu jabu ce, shi ya sa muka rushe wajen.

Ba iya nan muka tsaya ba, za mu yi amfani da sashe na 15 na dokar KNUPDA kuma za mu ci tarar kowanensu Naira 10,000, ko zaman gidan yari ko kuma duka biyun. Don haka muna neman su domin su biya kuɗin matsalolin da rushe wurin ya haifar.”

DailyTrust

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here