Umarnin shigo da kayan abinci yan Najeriya ke bukata – Kungiyoyin Arewa ga Tinubu

0
206
Tinubu
Tinubu

Shugaban hadakar kungiyoyi masu zaman kansu na Arewacin Najeriya Amb. Ibrahim Waiya yace Umarnin shigo da kayan masarufi daga iyakokin kasar Najeriya shi ne abunda al’ummar Najeriya ke buƙata sama da komai a halin yanzu.

Amb. Ibrahim Waiya ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da wata mai dauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Bashir A Bashir.

Amb. Waiya yace shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bada dama a shigo da kayan abinci domin shi ne hanya ɗaya tilo da al’ummar Najeriya zasu samu sami sassauci a yanayin da ake ciki na halin yunwa da sauran sace-sace da ake fama dashi na dalibai a kasar nan.

A makon daya gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin bude iyakokin Najeriya da jamhoriyar Nijar domin cigaba da harkokin mu’amala ta yau da kullum.

Sai dai a wani karin haske da mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Abdulaziz Abdulaziz ya yi yace bude iyakokin Najeriya baya nufin bada damar shigo da kayan masarufi cikin Kasar, wanda yan kasa suke zato.

“Har yanzu shugabannin Najeriya suna amfani ne da shinkafar ƙasar waje a gidajen su amma sun hana talakan kasa samun ta waje sun ce sai dai ya noma yaci”. A cewar Waiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here