Sojoji sun hallaka yan bindiga a Kaduna da Katsina

0
204

Dakarun sojojin Najeriya sun kashe wasu ‘yan bindiga huɗu a wani samame da suka kai jihohin Kaduna da Katsina.

Sanarwar da Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce sojojin sun kuma dakile yunkurin yin garkuwa da shugaban makarantar firamare a jihar Filato.

Sanarwar ta ce, bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa ana amfani da hanyar Gwamtu – Duduwa-Kujeni da ke karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, wajen kai wa ƴan bindiga kayaki a dajin Rijana, sai sojoji suka yi wa wajen kwanton bauna, inda suka hallaka biyu daga cikin ƴan bindigar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, a wani samame da sojoji suka yi nasarar kai wa a maɓoyar ‘yan bindiga da ke Dutsen Kura a karamar hukumar Batsari na jihar Katsina, sun yi nasarar kashe guda biyu, bayan musayar wuta da su.

Sanarwar ta kuma ce, a samame da aka kai jihar Filato, sojojin sun dakile yunkurin yin garkuwa da wani Mista Solomon Zakka, shugaban makarantar Pilot Primary School, Daffo, wanda aka so yin garkuwa da shi a gidansa da ke kauyen Maiduna a karamar hukumar Bokkos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here