Mafarauta da ƴan banga sun kashe ƴan bindiga 30 a Taraba

0
124
Ƙungiyar haɗin gwiwa ta mafarauta da yan banga na ci gaba da samun nasara a fafatawar su da ‘yan bindiga masu tayar da kayar baya a jihar Taraba.
Yayin da rashin zaman lafiya ke ci gaba da addabar wasu yankunan arewacin Najeriya, wasu al’umomi a jihar Taraba sun dauki matakin shawo kan lamuran tsaro, ta hanyar hada taro da sisi don daukar nauyin mafarauta sun tunkari lamarin.
Jihar Taraba na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar ‘yan bindiga dake kai wa al’umomin yankunan hare-hare, baya ga haddasa asarar rayuka, su kan kwashi dukiya ko barnatawa tare da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa.
VOA Hausa ta rawaito cewa, a yunƙurin neman dawo da zaman lafiya kungiyar hadin gwiwar mafarauta da ‘yan banga, an sama da ‘yan bindiga talatin a yankin Garbabi dake karamar hukumar Gashaka a jihar Taraba.
Alhaji Ibrahim Nanaye sarkin Fulanin Garbabi, shi ne ya jagoranci aikin kawo ƙarshen ƴan bindigar, ya ce baya ga kashe sama da talatin sun tarwatsa wani sansanin ‘yan bindigar da su ka hana mazauna yankunan zaman lafiya.
Hakimin garin Garbabi, Salihu Abbas Muhammad, ya tabbatar da cewa ba za su zauna ba har sai zaman lafiya ya dawo, dalilin da ya sa kenan suka tashi tsaye don kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar baki daya.
Mazauna yankin sun nuna farin cikinsu game da aikin hadin gwiwar da yanzu haka yake samar da sakamako mai kyau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here