An hallaka sojojin Najeriya 16 a jihar Delta

0
189

Babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa sojojin ƙasar 16, ciki har da kwamandansu a jihar Delta.

Bayanai na cewa jami’an sojoji da an kashe sojojin ne a ranar Alhamis, 14 ga watan Maris.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, mai magana da yawun Hedikwatar Tsaron Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya ce an kashe sojojin ne lokacin da sojojin runduna ta 181 ta Amphibious Battalion ke aikin samar da zaman lafiya a karamar hukumar Bomadi na jihar ta Delta.

Janar Tukur Gusau ya ce sun sanarwa gwamnatin jihar ta Delta faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa babban hafsan sojin ƙasar ya ce a gaggauta nemo waɗanda suka aikata kisan domin su fuskanci hukunci.

A cewarsa, an kama wasu waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Ya kuma ƙara nanata zimmar sojojin ƙasar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da da kuma tsaro a sassan ƙasar daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here