Wike ya kuduri aniyar ci gaba da rushe-rushe a Abuja

0
156
Nyesom-Wike
Nyesom-Wike

Sabon Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike ya sha alwashin dawo da martabar birnin, ta hanyar rusa gidajen da suka saba ka’ida tare da tabbatar da cewar ba a ci gaba da gine-gine ba bisa ka’ida ba.

Yayin da yake jawabi ga manyan jami’an ma’aikatar Abujan jim kadan bayan rantsar da shi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, Wike ya ce manyan abubuwan da zai mayar da hankali a kai, su ne batun tsaron birnin da kuma inganta shi wajen ganin ya yi gogayya da takwarorinsa na duniya.

Ministan ya kuma jaddada aniyarsa ta rusa duk wani gini da ya saba wa tsarin da aka yi wa birnin, koda kuwa wane babban mutum ne ya mallake shi.

Wike ya ce ba zai lamunce da yadda wasu shafaffu da mai ke gine-gine ba bisa ka’ida ba, yayin da gwamnati ta dora alhakin kula da birnin a hannunsa, saboda haka zai kaddamar da shirin rusa duk wani gini da aka yi a wurin da bai kamata ba da wadanda aka yi ba bisa ka’ida ba.

Ministan ya kuma gargadi wadanda aka bai wa filaye amma suka ki gina su, inda yake cewa zai yi amfani da ofishinsa wajen kwace irin wadannan filaye domin bai wa wadanda suke bukata.

Wike ya ce a karkashin jagorancinsa, duk wanda za a bai wa fili a Abuja, sai ya bayyana lokacin da zai gina shi domin zama shaidar daukar mataki a kansa idan ya saba alkawari.

A karshe ministan ya janyo hankalin mazauna birnin a kan muhimmancin biyan harajin gidaje da doka ta tanada domin bai wa hukumomi damar gudanar da ayyukan da za su inganta birnin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here