Gwamnatin Jigawa tana cigabada gyaran hanyoyi da ruwan sama ya lalata

0
129

Gwamnatin jihar jigawa tace tana bakin kokarinta wajen gyaran hanyoyi da kwalbtoci da ruwan sama ya karya domin baiwa masu ababan hawa da sauran al’umma damar yin zurga-zurga.

Babban sakatare a ma’aikatar aiyuka da sufuri ta jiha, Injiniya Datti Ahmed ne ya sanar da hakan ga manema labarai a dutse.

Ya ce a yanzu haka gwamnati ta kai kayayyakin aiki domin gyaran hanyar Baranda da ta lalace sakamakon mamakon ruwan saman da ake samu a daminar bana.

Injiniya Datti Ahmed ya kara da cewar gwamnati ta gyara wuraren da ruwa ya yi ta’adi akan hanyar Jahun zuwa Gujungu, yayin da ya bayyana gyaran da ake akan hanyar Kiyawa zuwa Jahun, ruwa saman ya hana su aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here