Sai nan da shekara 3 za mu bada mulki – Abdulrahmane Tchiani

0
206

Shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Janar Abdulrahmane Tchiani, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da tafiyar da gwamnatinsu ta rikon kwarya har sai nan da shekaru uku masu zuwa kafin su mika mulki ga farar hula.

Ya kuma yi gargadin cewa duk wanda ya kuskura ya kaddamar da kai wa kasarsa hari sai ya yi da-na-sani.

A cikin wani jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin din kasar a ranar Asabar, Tchiani ya ce,

“Babban burinmu shi ne mu kwace mulki, kuma duk wanda ya sake ya kai mana hari zai gane shayi ruwa ne.”

Gargadin nasa na zuwa ne kwana ɗaya bayan dakarun Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS), sun ce a shirye suke su kutsa kai Nijar domin su dawo da mulkin Dimokuraɗiyya a Nijar.

A cikin jawabin mai tsawon minti 12, Tchiani ya kuma cewa, “Muna sanar da kafa wani kwamitin tattaunawa na kasa da zai fito da nagartattun hanyoyin samar da sabon Kundin Tsarin Mulki.”

Kazalika, ya yi jawabin ne jim kadan bayan da tawagar ECOWAS karkashin tsohon Shugaban Najeriya, Abdulsalami Abubakar, ta gudanar da tawagar ta kuma sami ganawa da hambararren Shugaban na Nijar, Mohammed Bazoum. domin warware rikicin siyasar kasar a birnin Yamai.

Tawagar ta kuma sami ganawa da hambararren Shugaban na Nijar, Mohammed Bazoum.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here