Matsin rayuwa: Magidanci ya rataye kansa har lahira a Jigawa

0
180

Wani magidanci ya rataye kansa har lahira sakamakon tsadar rayuwa da matsanancin talaucin da suka addabe rayuwarshi a Jihar Jigawa.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam ya baiyanawa manema labari cewa magidancin mai shekaru 35 ya rataye kansa ne har lahira a wani kauyen Dungun Tantama da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa ta jihar.

Shisu ya bayyana cewa da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar ta samu mummunan labarin.

Ya ce jami’an rundunar ne suka kwance gawar magidancin daga cikin bishiyar da aka gano ta a rataye, suka kai ta asibiti domin gudanar da bincike

DSP Shiisu ya bayyana cewa rundunar ta samu labarin cewa tun ranar Laraba da ta gabata magidancin ya fice daga gidansa ba tare da an san inda ya tafi ba, sai daga bisani a gano gawarsa rataye a jikin bishiyar.

A cewarsa bincike ya nuna magidancin ne ya rataye kansa da kansa, saboda matsin rayuwa da tsananin talauci da suka sa shi gaba.

Tuni dai aka sallama gawarsa ga iyalansa don yi masa jana’iza

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here