Makasudin hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya – NBS

0
225
Kayan Abinci

‘Yan Najeriya sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan sabon rahoton hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci da hukumar kididdiga ta kasar, NBS ta fitar a ranar Talata.

A sabon rahoton da hukumar ta fitar ta ce hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 24.08 cikin 100 a watan Yuli daga kashi 22.79 cikin 100 na watan Yuni.

Hakan na nufin an samu karin kashi 1.29 cikin wata daya kan farashin kayayyaki. Farashin abinci kuwa ya karu da kashi 1.73 daga kashi 25.25 cikin 100 a watan Yuni zuwa kashi 26.98 cikin 100 a watan Yulin 2023.

Hakan na nufin an samu karin kashi 1.29 cikin wata daya kan farashin kayayyaki. Farashin abinci kuwa ya karu da kashi 1.73 daga kashi 25.25 cikin 100 a watan Yuni zuwa kashi 26.98 cikin 100 a watan Yulin 2023.

Kazalika farashin kayan abincin daga watan Yulin 2022 zuwa Yulin 2023 ya karu da kashi 4.97 daga kashi 22.02% a Yunin 2022 zuwa 26.98% a Yunin 2023.

Mutane da dama sun koka kan wannan lamari wanda masana ke cewa idan har hukumomi ba su dauki wasu matakai da suka dace ba, to lamarin ka iya ci gaba da ta’azzara.

Masu sharhi na danganta wannan hauhawa da tsarin Babban Bankin kasar na kara kudin ruwa a watan Yuli, daga kashi 18.5 zuwa 18.7 cikin 100.

Sannan janye tallafin man fetur da aka yi ma ya yi tasiri sosai wajen ta’azzara farashin kayayyakin.

Abubuwan da hauhawar ta shafa
NBS ta wallafa jerin abubuwan da hauhawar ta shafa kamar haka:

Kayan abinci da lemuka – 12.47%
Gidaje da ruwa da wutar lantarki, gas da sauran dangin fetur – 4.03%
Kayan sawa da takalma – 1.84%
Sufuri – 1.57%
Kayan gado da kayan gida – 1.21%
Ilimi – (0.95%)
Lafiya – 0.72%
Sauran ayyuka – 0.40%
Gidajen abinci da otel-otel – 0.29%
Barasa da sigari da goro – 0.26%
Sadarwa – 0.16%.
Jihohin da abinci ya fi tsada

Kayan abincin da farashinsu ya fi karuwa daga Yunin 2022 zuwa Yunin 2023 kuwa su ne mai da burodi da kifi da dankali da doya da kayan marmari da nama da ganyayyaki da madara da kuma kwai.

Haka kuma NBC ta ce jihohi uku ne farashin kayan abinci ya fi tsada daga watan Yunin bara zuwa Yunin bana, da suka hada da Kogi da Lagos da Ondo, yayin da jihohin Borno da Jigawa da Sokoto kuma su ne farashin abinci bai ta’azzara sosai ba.

Kogi da Abia da Akwa Ibom kuma su ne jihojin da farashin kayan abinci ya fi hauhawa a cikin wata dayan da ya gabata, wato daga Yuni zuwa Yuli, su kuwa jihohin Jigawa da Taraba da Yobe su ne farashin abinci bai faye hawa da sauri ba kamar sauran a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here