Najeriya: Halin da talaka yake ciki kan tsadar rayuwa

0
244

Babban abunda yake tayar wa da talakan Najeriya hankali cikin wannan rayuwar shine yadda mutum zai tashi ya fita fafutuka ya samo abunda zai rayu dashi na yau da kullum, sannan daga bisani kuma idan ya koma washe gari sai ya tarar farashin kayan ya kara tashi.

Wadansu mutanen ma a yanzu sun hakura da tsohon tsarin nan na cin abinci sau 3 a rana duba da irin yadda rayuwar tayi tsada a yau da kuma yadda ake yi wajan samun abinda za a ci da kyar.

Bangaren ilimi, dalibai musamman masu karantar fannin lafiya suna kokawa matuka bisa yadda karin kudin makaranta yasa su cikin zullumin yin adabo da karatun nasu.

Lamarin da ya kara bayar da tsoro ma shine yau antashi cikin rade-radin cewa farashin man fetur zai kuma tashi, wanda aka ce tashinsa da saukarsa ya dogara ne kacokan a kan tashi da kuma faduwar Dala.

Farashin Dala kuwa kullum tashi yake tamkar tashin cilakowa ci ranin tashi, sai dai ai ta ganin tashinta amma ba za a ga saukowarta ba.

HAUSA24 ta tattauna da Abubakar Ibrahim, magidanci da yake fadi tashi wajen kula da iyalansa ya nuna damuwar sa kan yadda halin tsadar rayuwa yake kara tabarbarewa a Najeriya.

A kalaman Ibrahim ya ce ”talakafa ba ya da wani gata a kasara nan face idan yana da hankali dauki carbi watakila ya dace ranar gobe kiyama”

”Yanzu sanatoci da yan majalisu za su iya siyawa kansu motoci har na Naira biliyan 140 a irin wannan halain da ake ciki, amma shi talaka fa? ta abinci yake. Wannan kudin basu iso kowa ya ci abinci ya shiga cikin arziki ba a Najeriya? Anya akwai imani awajen nan kuwa?

Wahalar rayuwa ta saka garin rogo na Naira 30 ya gagari mutum bai da kudin siya wannan rayuwa har ina” acewar Ibrahim

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here