Rikici ya sake barkewa a wasu biranen Sudan

0
231
Sudan

Rikici ya barke a birnin Nyala da ke yammacin Sudan da sauran wurare a kudancin yankin Darfur, kamar yadda wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ana fargaɓar faɗan zai iya yaɗuwa zuwa ilahirin yankin na Darfur da ke yammacin ƙasar.

Rikicin da ake yi a birnin Khartoum ya haifar da hare-haren ƙabilanci a yammacin Darfur, tare da raba sama da mutum miliyan huɗu da muhallansu zuwa makwabtan ƙasashen Chadi da Masar da Sudan ta Kudu da sauran ƙasashe.

A baya birnin Nyala – birni na biyu mafi girma a Æ™asar – ya fuskanci faÉ—an da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF.

FaÉ—an na baya-bayan na ya lalata ababen more rayuwa kamar lantarki da ruwan sha da kuma hanyoyin sadarwa a birnin na Nyala, kamar yadda Reuters ya ruwaito.

Kungiyar lauyoyin Darfur, mai sa ido kan hakkin bil-adama ta ce aƙalla mutum takwas ne suka mutu sakamakon faɗan na baya-bayan nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here