Za mu tura kwamiti na musamman zuwa Nijar – ECOWAS

0
267

Majalissar kungiyar ECOWAS ta yammacin Afrika na nazarin tura wani kwamiti na musamma zuwa Nijar domin ganawa da shugabannin gwamnatin sojin kasar da suka yi juyin mulki a watan da ya gabata.

Wannan na zuwa ne, daidai lokacin da gwamnatin sojin kasar ke ci gaba da bijirewa matsin lamba ta diflomasiyya game da maido da mulkin farar hula, kamar yadda kakakin majalisar ya bayyana a ranar Asabar.

Kungiyar ta Ecowas ta amince da aiwatar da Shirin ko ta kwana, don maido da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, inda babban jami’in diflomasiyyar EU ya nuna damuwarsa game da yanayin da ake tsare da shi tun bayan da jami’an tsaronsa suka hambarar da shi a ranar 26 ga watan Yuli.

An shirya taron shugabannin hafsoshin kasashen kungiyar ta yammacin Afirka ranar Asabar a Accra babban birnin kasar Ghana, said ai daga bisani kungiyar ta fitar da sanarwar cewa an dage wannan taro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here