Kakan da ya sayar da jikarsa jaririya ya shiga hannu

0
118

’Yan sanda a Jihar Oyo sun kama wani mutum mai suna Monday Chukwuka da ake zargin ya sayar da jikarsa jaririya a kan kudi Naira dubu 700.

Da yake yi wa ’yan jarida holen mutumin a wannan Asabar a ofishinsa da ke Eleyele a Ibadan, Kwamishinan ’yan sandan Oyo, CP Adebola Hamzat ya ce “bayanan sirri da muka samu ne ya kai ga kama mutumin a garin Ibafo a Jihar Ogun.

“Bayan bincike mutumin ya tabbatar da cewa ya sayar da jaririyar mai kwana daya da haihuwa da wani kamfanin kyankyasar jarirai da ke Obehi a Okwa ta Yamma a Jihar Abia.”

Kwamishinan ya ce bayan kama Kakan jaririyar sun bi sawu zuwa wannan Kamfani inda suka yi nasarar kama mutane 5 wadanda suka sayi jaririyar a hannun kakan nata.

Daya daga cikin ababen zargin ya shaida wa ’yan jarida cewa an ba shi la’adar Naira dubu 50 saboda kulla cinikin jaririyar.

Da yake amsa tambayar manema labarai, Monday Chukwuka ya furta da bakinsa cewa ya yanke shawarar dauke jikarsa daga hannun uwarta mai-jego saboda a cewarsa ya san ba zai iya daukar dawainiyar uwar da jaririyar ba.

“Dalili kenan da ya sa na sayar da jaririyar ga Kamfanin kyankyasar jarirai da na yi amfani da kudin wajen biyan kudin hayar shago da sayen wasu kaya.”

Ita ma matarsa mai suna Sarah cewa ta yi ba ta da masaniya a kan cinikin jaririyar da mijinta ya kulla.

Sai dai ta ce a lokacin da mijinta ya zo karbar jaririyar ya shaida mata cewa zai kaita inda za a yi mata kyakkyawar reno har zuwa shekara 2 da zai dawo da ita gare su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here