Juyin Mulki: An tsaurara matakan tsaro a iyakar Najeriya da Nijar

0
223

Jami’an tsaron Najeriya sun tsaurara matakai a iyakar kasar da Nijar a bayan kungiyar ECOWAS ta umarci dakarunta su yi shirin ko-ta-kwana domin zuwa su murkushe sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar. 

RFI  ta ruwaito cewa a Karamar Hukumar Illela ta Jihar Sakkwato da ke kan iyakar kasashen biyu, cewa jami’an tsaron Najeriya sun tsaurara da yin sintiri a yankin.

Mazauna yankunan da ke kai-koma tsakanin Najeriya da Nijar sun bayyana cewa a jami’an tsaron Najeriya sun fara sintiri a wuraren da ba su saba yi ba a baya, a tsakannin kasashen biyu, matakin da suka ce yana kara musu natsuwa.

Mazaunan garin Illela sun bayyana cewa yanzu sojojin Najeriya da ke tsaron iyakar sun koma yin sintiri, sabanin yadda suka saba yi a baya.

Hakan kuwa kari ne a kan rufe iyakokin kasashen biyu, wanda Najeriya ta fara yi tun shekarun da suka gabata, kafin masu juyin mulkin Nijar su rufe bangarensu.

Juyin mulkin ya kawo tsamin dangantaka tsakanin manyan makwabtan biyu, duk da cewa akwai dubban ’yan Najeriya da ke zaman gudun hijira a Nijar sakamakon rikicin Boko Haram.

Najeriya mai jagorancin ECOWAS ta yanke wutar lantarkin da ta fi kowa ba wa Nijar, domin matsa wa masu juyin mulkin su koma bariki, Shugaba Mohamed Bazoum ya ci gaba da mulki.

Daga baya sojojin suka katse hulda da ita, suka kuma ki sauraron wakilan kungiyar ECOWAS da shguaban Najeriya Bola Tinubu ya tura domin tattaunawa da su.

Zuwa yanzu dai Najeriya ba ta sanar da matakin sojin da za ta dauka a kashin kanta game da lamarin na Nijar ba, duk da cewa tana daga cikin kasashen ECOWAS da suka yanke shawarar tura dakaru.

Amma Kwaddibiwa, daya daga cikin kasashen da ke makwabtaka da Nijar, ta sanar cewa za ta tura sojoji 1,ooo domin aiki a rundunar ECOWAS da za ta yi aikin dawo da mulkin farar hula a Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here