Za mu kashe Bazoum idan aka kawo mana hari — Masu juyin mulki

0
205
A woman holds the image of ousted Niger President Mohamed Bazoum, 63, who has been held by coup plotters with his family in his official Niamey residence since July 26, during a protest outside the Niger Embassy, in Paris on August 5, 2023. - A West African delegation failed to secure the return to power of Niger's elected government on August 4, 2023, despite proposals to resolve the crisis as the junta curtailed military cooperation with former colonial power France. Pressure on the leaders of a coup in Niger mounted on August 5, 2023, on the eve of a west African bloc's deadline for the military to relinquish control or face possible armed intervention. (Photo by STEFANO RELLANDINI / AFP)

Masu juyin mulkin Nijar sun yi barazanar kashe shugaban kasar da suka hamɓarar, Mohamed Bazoum, da ke hannunsu, muddin ƙungiyar ECOWAS ta kai wa ƙasar hari.

Sojojin sun yi gargadin ne a yayin da majalisar shugabannin ƙasashen ECOWAS ta umarci kwamitin manyan hafsoshin tsaron ƙungiyar ya tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Nijar domin ɗaukar matakin soja ba tare da bata lokaci ba domin dawo da Bazoum kan kujerarsa.

ECOWAS ta ce daukar matakin sojin ya zama dole, bayan sojin sun bijire wa duk wani yunkurin tattaunawa da aka nemi yi da su.

Sai dai Sakataren gwamnatin Amurka, Anthony Blinken, wanda ya bayyana cewa ya fi goyon bayan sasantawa da masu juyin mulkin maimakon daukar matakin soji.

Blinken ya lashe amansa ne bayan da farko ya sanar cewa Amurka na goyon bayan duk matakin da ECOWAS za ta dauka a Nijar domin dawo da Bazoum kan kujerarsa.

Kwararru da daidaikun ’yan Najeriya dai sun yi tir da matakin na ECOWAS, wanda suke bayyana cewa zai kara rura wutar fitinar tare da kuma yin illa musamman ga Arewacin Najeriya, babbar makwabciyar Nijar, wadda kuma dubban ’yan kasarta da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu ke zama gudun hijira a can. Don haka abin da a fi dacewa shi ne tattaunawa.

Kungiyar kare muradun Arewa (ACF) da Jama’atu Nasril Islam na daga cikin wadanda suka bukaci a yi amfani da hanyar diflomasiyya wajen warware rikicin na Nijar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito wani jami’in Amurka na cewa sojojin na Nijar sun yi barazanar kashe Bazoum idan ECOWAS ta auka musu ne a tattaunawarsu da Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Victoria Nuland da ta ziyarci kasar.

Gabanin haka, Bazoum ya sanar a wata wasika da ya aike wa abokinsa cewa azabar da yake sha a hannun sojojinta kai ga yanzu gayar shinkafa yake ci. Amurka da Majalisar Dinkin Duniya ke bayyana damuwa kan halin da hambararren shugaban yake ciki a tsare, mako biyu bayan kifar da gwamnatinsa.

A ranar da ECOWAS za ta yi taron yanke shawarar kan matakin sojin ne gwamnatin sojin na Nijar din ta nada ministoci 21, ciki har da hafsoshin soji.

Shugabannin kasashen sun yi zaman a Abuja ranar Alhamis ne bayan Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya a Yammacin Afirka Malam Muhammadu Sanusi II ya zama mutum na farko da ya gana da masu shugaban juyin mulkin, Janar Abdourahmane Tchiani, bayan da farko sojojin sun ki tattaunawa da wakilan ƙasashen duniya da na ECOWAS da ta yi kurarin far musu da yaƙi idan ba su miƙa wa Bazoum kujerarsa ba.

Bayan ganawar Sanusi II ya bayyana cewa Janar Tchiani ya ba shi muhimmin sako ga shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, inda bayan dawowarsa Abuja suka yi ganawar sirri da Tinubun a Fadar Shugaban Kasa.

Gabanin zaman nasu, Majalisar manyan malaman Musulunci da takwarorinsu Kiristoci sun ziyarci Tinubu da ke jagorantar ECOWAS inda suka nemi ya jingine batun matakin soji a kan masu juyin mulkin, saboda illar da hakan za ta yi ga Najeriya, babbar maƙwabciyar Nijar.

Tun da farko Majalisar Dokokin Najeriya ta buƙaci hakan daga gareshi, bayan da ya ba wa masu juyin mulkin wa’adin komawa bariki su miƙa mulki ga Bazoum, in ba haka ba ECOWAS na iya ɗaukar matakan soji a kansu.

Sojojin Nijar din dai sun jima da yin watsi da gargadin na ECOWAS, inda suka ce za su yaki duk wanda ya nemi auka wa kasarsu, ko yi mata shisshigi.

Hasali ma sun rufe sararin samaniyar kasar, da kuma iyakarsu da Najeriya, sannan suka samu goyon bayan yakar duk wanda ya nemi yi musu shissishigi, daga makwabtansu, kasashen Mali da Burkina Faso da Guinea Busssau inda sojoji suka yi juyin mulki.

Najeriya dai ta yanke wutar lantarkin da take ba wa Nijar domin matsa wa masu juyin mulkin, wadanda kuma martaninsu suka katse hulda da ita, duk da cewa akwai ’yan Najeriya da ke zaman gudun hijirar a can.

Tuni ECOWAS ta sanya wa gwamnatin sojin takunkumin karya tattalin arziki, a yayin da manyan kasashen duniya da ke dasawa da Nijar a zamanin Bazoum, Amurka da Faransa da Italiya suka janye tallafinsu a kasar. Haka ma Majalisar Dinkin Duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here