Me ya sa tsofaffin taurarin Kannywood ke yawan neman taimako?

0
313

Jama’a da dama na mayar da martani kan yadda ake yawan samun tsofaffin taurarin fina-finan Kannywood da ke fitowa fili suna neman taimako sakamakon matsalolin rayuwa da suka fada a ciki.

Na baya-bayan nan shi ne yadda fitaccen dan wasan kwaikwayo na Hausa Abdullahi Shuaibu, wanda aka fi sani da Karkuzu, ya nemi jama’a su taimaka masa sakamakon lalurar makanta da yake fama da ita.

A wata hira da ya yi da Zinariya TV, ya bayyana cewa yanzu haka abinci na neman gagarar sa haka kuma tuni ya makance kuma ga shi ba shi da matsuguni.

Wannan lamari ya yi matukar jan hankalin jama’a a shafukan sada zumunta inda ake ta muhawara.

Hakan ne ma ya sa shahararren dan wasan kwallon kafa na Nijeriya Ahmed Musa ya ba shi naira dubu dariya biyar da yi masa alkawarin saya masa gida da ya kai na naira miliyan biyar.

Dalilin da ya sa taurarin ke yawan neman taimako

Masana da masu tsokaci kan harkokin Kannywood sun bayyana dalilai da dama da suke gani ke sa wa tsoffin taurarin fina-finan Hausa suke shiga mawuyacin hali da kan kai su ga neman taimako.

Dakta Muhsin Ibrahim, Malami a Cibiyar Nazari kan Afirka da ke Jami’ar Cologne ta kasar Jamus, ya shaida wa TRT Afrika cewa mawuyacin halin da ‘yan wasan Hausa ke shiga na da nasaba da abubuwa uku.

Rashin tsari

Malamin Jami’ar ya bayyana rashin tsari a masana’antar Kannywood a matsayin abu na farko da yake jawo wannan matsalar.

“Dama masana’anta ce da ake tafiyar da ita babu tsari, don haka babu wata kwantiragi da mutum ke sanya hannu idan zai yi fim ko wani tanadi alal misali da za a iya sakawa a wani asusu,” in ji Dakta Muhsin.

Ya kara da cewa: “Babu wasu tsare-tsare kamar na fansho yadda idan girma ya cimma mutum ko rashin lafiya ko mutuwa zai iya amfana ko iyalansa su amfana da wani fansho ko giratuti, baki daya babu wannan tsarin.”

Masanin ya ce ana tafiyar da masana’antar ne a tsarin ‘zo ka yi mini aiki na ba ka kudi’.

Rashin tanadi

Dakta Muhsin ya bayyana cewa a wannan bangaren ‘yan wasan na Kannywood sun rabu gida biyu.

“Wasu daga cikinsu da Allah ya yi musu daukaka sun samu kudi da yawa daga karshe sai su yi tunanin kamar wannan rayuwar za ta dore sai su ki tanadi.

“Da yawa kuma ba sa iya yin tanadi domin kuwa a gaskiya Kannywoo industry ce da yawanci kudin sayen abinci ake samu kawai. Shi ya sa lokacin da tauraruwarsu ta daina haskawa ko rashin lafiya ya same su ko girma ya cimma su, sai abubuwa su dagule,” in ji shi.

Rashin hadin kai

A cewar Dakta Muhsin, duk masana’antu wadanda suke da tsari da suka hada da makarantu ko bankuna ko kafafen watsa labarai ko ma’aikatu, akan samu rayuwa ta juya wa wani baya saboda asara ta rayuwa ko rashin lafiya.

“Idan akwai hadin kai, za a hadu ne a taimaka wa wanda irin wannan matsalar ta faru da shi, ba sai na waje ya ji ba. Amma saboda Kannywood ba su da hadin kai shi ya sa ba sa iya magance irin wadannan matsalolin sai an fito cikin duniya an sanar,” in ji shi.

Dakta Muhsin ya yi gargadin cewa akwai bukatar masu tasowa a harkar fim su koyi darasi kan wadannan abubuwan da ke faruwa.

‘Yan Kannywood da suka taba shiga mawuyacin hali

Akwai taurarin fina-finan Kannywood da dama da suka fito fili suna neman taimako sakamakon wata matsala da suka shiga ta rayuwa.

Akasarin taurarin sun yi fice a fina-finansu na baya, kuma neman taimakon da suka yi ya jawo ce-ce-ku-ce matuka ga masana’antar Kannywood.

Bashir Bala Ciroki

Bashir Bala ya samu tallafin kudi daga jama’a. Hoto/Others

A kwanakin baya, Bashir Bala Ciroki ya koka cewa an daina saka shi a fim abin da a cewarsa ya jefa shi cikin halin matsi na rayuwa.

Ya bayyana cewa matsin da ya shiga ya sa ya koma sayar da kunun zaki domin ciyar da iyalinsa.

Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a a lokacin wanda hakan ya sa aka kafa gidauniya domin tara masa kudi.

Shafin Northern Hibiscus a Instagram ya tara masa kimanin naira 215,000 domin tallafa masa.

Sani Idris Moda

Moda ya shafe shekaru yana fama da ciwo wanda har daga baya aka yanke masa kafa. Hoto/Others

Sani Idris Moda tsohon fitaccen dan wasan Hausa ne wanda ya yi suna a fim din Wasila.

Tsakanin shekarar 2018 zuwa 2021, an ta tattauna wa a kansa a shafukan sada zumunta bayan an rinka yada hotunansa ana neman taimako sakamakon wata rashin lafiya da ya yi da ta kai ga yanke masa kafa.

Kafin yanke kafarsa, har jita-jita aka yada kan cewa ya rasu. Moda ya bayyana cewa ya shafe shekaru da dama yana fama da ciwon suga.

Tahir Fagge

Tahir Fagge ya sha fama da ciwon zuciya wanda har ya soma rawa a gidan gala domin samun kudin magani. Hoto/Others

A kwankin baya an yi ta ganin bidiyoyin Tahir Fagge yana rawa a gidajen Gala.

Wannan batu ya yi matukar tayar da hankalin jama’a da kuma jawo ce-ce-ku-ce.

Sai dai tsohon tauraron na fina-finan Hausa ya bayyana cewa rashin lafiya da kuma mawuyacin halin rayuwa ne suka sa yake zuwa yana yin wannan rawa.

Ya bayyana cewa yana yin rawar ne domin samun kudin da zai saya wa kansa maganin ciwon zuciyar da yake fama da shi.

Marigayi Sani SK

Sani SK ya rasu a Disambar 2021 bayan fama da doguwar rashin lafiya. Hoto/Ali Nuhu Channel

Shi ma Marigayi Sani Garba SK ya shiga mawuyacin hali kafin rasuwarsa sakamakon ciwon suga da hawan jini.

Sani SK na daga cikin taurarin Kannywood na farko-farko wanda ya yi fina-finai da dama kuma ya yi suna.

Fim din Badali na daga cikin wanda ya daga marigayin ya yi suna. Ya yi fama da doguwar jinya kafin rasuwarsa inda aka yi ta yawo da bidiyoyinsa a shafukan sada zumunta.

A lokacin da yake fama da tsananin rashin lafiya, ya dauki wani bidiyo inda ya yi kira ga masoyansa da su agaza masa kan halin da yake ciki na rashin lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here