Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 33 a China

0
171

Hukumomi a birnin Beijing, sun ce an tabbatar da mutuwar mutane 33 sakamakon wata ambaliyar ruwa a babban birnin China ya fuskanta a makon da ya wuce.

Hukumomin sun ce har yanzu ana neman wasu mutane 18 da ba a san inda suka shige ba.

Guguwar dai ta daidaita birnin Beijing, inda ta dangana da lalata Arewa Maso Gabashin gundumar Jilin.

Gwamnatin China ta girke dubban sojoji da jamai’an sa kai a Jilin, daidai lokacin da ake sa ran guguwar Doksuri na gab da isa can, tuni kuma aka kwashe dubban mutanen da ke zaune a yankin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da irin wannan ambaliya ta afku a yankin ba.

Sai dai gwamnati na ci gaba da daukar matakai don hana salwantar rayuka da duniyoyin jama’ar gundumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here