Muhammadu Sanusi na II ya gana da shugaban Nijar Tchiani

0
177

Tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya gana da shugaban sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani a Yamai, babban birnin kasar.

Sun yi ganawar ce ranar Laraba a yayin da kasashen duniya ke ci gaba da kokarin ganin sojojin sun mayar da mulki ga Shugaba Mohamed Bazoum wanda suka kifar da gwamnatinsa a karshen watan jiya.

Bayanai sun ce Muhammadu Sanusi na II ya yi kokarin shawo kan Janar Tchiani ya sauya matsaya bayan da sojojin suka ki yin biyayya ga wa’adin da kungiyar ECOWAS ta ba su na komawa bariki.

Babu cikakken bayani game da wanda ya tura tsohon sarkin na Kano Yamai – ko kungiyar ECOWAS ce ko kuma ziyara ce ta kashin kansa.

Ziyarar tasa na zuwa ne a yayin da sojojin na Nijar suka hana jami’ai daga kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS da Majalisar Dinkin Duniya zuwa Jamhuriyar Nijar a yau Laraba.

Kazalika Muhammadu Sanusi na II ya je Yamai kwana biyar bayan tawagar da shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya aika Nijar don ganawa da sojojin ba ta yi nasara ba.

Tawagar, karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya Janar Abdulsalam Abubakar da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ba ta samu ganin Janar Tchiani da Mohamed Bazoum ba.

Ita ma mataimakiyar Saataren Harkokin Wajen Amurka, Victoria Nuland, wadda ta je Nijar a makon jiya, ta yi korafin cewa ba a bar ta ta gana da jagoran masu juyin mulkin ba.

A gefe guda, wani tsohon dan tawaye kuma dan siyasa a Jamhuriyar Nijar, Rhissa Ag Boula, ya kaddamar da wata kungiya da za ta yi fafutukar ganin an mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

Boula ya kaddamar da kungiya mai suna the Council of Resistance for the Republic (CRR) domin neman goyon baya daga kasashen duniya don mayar da tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Wannan wata alama ta nuna turjiya ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar a karshen watan jiya.

Kungiyar tana goyon bayan ECOWAS da sauran kungiyoyin kasashen duniya da ke neman ganin an mayar da Bazoum kan mulki, in ji sanarwar.

Rhissa Ag Boula, wanda tsohon minista ne a kasar, ya ce manyan ‘yan siyasar Nijar da dama sun shiga kungiyar CRR sai dai ba su fito sun bayyana ba saboda dalilai na tsaron lafiyarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here