Man Utd ta cimma matsaya da West Ham kan Maguire

0
184

Manchester United da West Ham United sun cimma yarjejeniyar cinikin dan wasa Harry Maguire. 

A satin da ya gabata ne, West Ham ta taya dan wasan mai shekara 30 a duniya a kan kudi fam miliyan 20 sai dai nan take Manchester United ta yi fatali da tayin, inda ta ke neman a bata fam miliyan 40.

Sai dai daga baya West Ham ta sake sabon tayi na fam miliyan 30 shi ma United ta ce ba za ta siyar a haka ba.

Da safiyar yau ne kuma, kungiyoyin biyu suka cimma matsaya a kan fam miliyan 30 din kuma yanzu dan wasan zai tattauna batun albashi da kungiyar da ke birnin Landan.

A 2019 ne Manchester United ta kashe fam miliyan 80 wajen sayen dan wasan daga Leceister City.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here