Malamai sun gargadi Tinubu kan daukar matakin soji a kan Nijar

0
167

Zauren Malaman Najeriya ya gargadi shugaban Nijeriya kuma shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu dangane da yunkurin daukar matakin soji a kan Jamhuriyar Nijar, biyo bayan hambarar da gwamnatin farar hula da sojoji suka yi.

Malaman sun ce matakin ba zai haifar da sakamako mai kyau ga kasashen biyu ba.

Malaman sun nemi kowane bangare da ya dauki matakin salama cikin yanayin diflomasiyya domin tallafawa Jamhuriyar Nijar da mutanenta.

Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da kungiyar ta yi, inda shugabanta Aminu Inuwa Muhammad, da sakatarenta Injiniya Basheer Adamu Aliyu da suka cimma a ranar Juma’a.

Sun yi fatan cewa majalisar dokokin Nijeriya ba za ta amince wajen bari a shiga cikin wannan rigimar ba wadda ka iya zama yaki.

Kazalika, malaman sun jawo hankalin malamai a dukkanin matakai da su dukufa wajen fadakarwa da jan hankali kan illar janyo fada tsakanin makwabta tare da tabbatar da dorewar alakar tsakanin Nijeriya da Nijar.

“Yana da kyau gwamnatin Nijeriya ta sake yin duba kan kokarin da ta ke yi, sannan kuma ga barazanar tsaro ta ko ina, wadanda su ke ta tatse ‘yar lalitar kasar, kada a afka mu cikin wani rikici da za mu iya kaucewa, kawai don mu farantawa wasu kasashen duniya a siyasance.”

Malaman da suka sanya hannu kan takardar a yayin zaman sun kai 25 daga sassa daban-daban na kasar nan, inda suka yi fatan cewa barazanar da ake gani a zahirance ba zai kai ga janyo barakar zaman lafiya a tsakanin Nijeriya da Nijar ba.

Zauren ya jadadda goyon bayan matakan diflomasiyya da a ka fara dauka ta hanyar aikewa da wakilai domin zama da jagororin sojin juyin mulkin Nijar don tattaunawa cikin salama.

“Juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar da ma duk wadanda a ka yi a sauran kasashen yankin SAHEL abun takaici ne, kuma ya cancanci duk masu ra’ayin dimokuradiyya su yi tir da shi da ma duk masu neman zaman lafiya a duniya.

“Duk da cewa mutane da dama na fifita dimokradiyya da tsare-tsarenta, amma hanyar samar da shugabanci na gari, abu ne da ya kebanci mutanen kowace kasa su kadai. Don haka damar mutanen Jamhuriyyar Nijar ce su bi duk hanyoyin da su ka ga sun dace domin dawo da dimokradiyya a kasarsu, idan sun ga hakan ya dace; kuma duk wani kokarin da wani zai yi, a ko ina yake, matukar ba mutanen Nijar ba, abu ne da zai yi karan tsaye ga dimokradiyya da sunan samar da dimokradiyya.”

Malaman sun ce wa’adin kwanaki bakwai da ECOWAS ta bai wa jagororin sojin kasar ya ci karo da tanade-tanaden dimokradiyya kuma shisshigi ne ga ‘yancin gudanar da kasa mai cin gashin kanta.

Sanarwar ta ce, kaso mafi rinjaye na al’ummar Nijeriya ba su goyon bayan yakar Nijar wadda ke da kyakkyawar alaka.

“Abin da ya fi wannan hatsari kuma, shiga wannan yaki zai jawo a mayar da wanan yankin namu wani zakaran gwajin dafi da za a yi amfani da shi wajen wasa kwanji da gwajin makamai, daga kasashen waje da ke da muggan manofofi ga wannan yankin.

“Kuma amfani da karfin soji zai haifar da wuce gona da iri game da babban aikin ECOWAS na samar da tsaro da kariya daga kasashen waje, ya ba da dama ga wasu su sa muke fada da juna.”

Malaman da suka sanya hannu a sanarwar sun hada da Malam Aminu Inuwa Muhammad, Jagora, Kano; Prof. Mansur Ibrahim Sokoto mni, Mamba, Sokoto; Dr. Bashir Aliyu Umar, Mamba, Kano 04 Dr. Sa’id Ahmad Dukawa, Mamba, Kano; Dr. Abubakar Muhammad Sani B/Kudu, Mamba, Jigawa; Dr. Khalid Abubakar Aliyu, Mamba, Kaduna; Prof. Muhammad Babangida Muhammad, Mamba, Kano; Prof. Salisu Shehu, Mamba, Bauchi; Prof. Ahmad Bello Dogarawa, Mamba, Kaduna; da kuma Mal Ahmad Bello Abu Maimounah, Mamba, Katsina.

Sauran su ne: Dr. Muhammad Alhaji Abubakar, Mamba, Borno; Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sokoto, Mamba, Sokoto; Malam Aminu Aliyu Gusau, Modibbon Gusau, Mamba, Zamfara; Mal Shehu Muhammad Maishanu, Mamba, Zamfara; Prof Muhammad Amin Al-Amin, Mamba, Katsina; Barrister Ibrahim Muhammad Attahir, Mamba, Gombe; Dr. Salisu Ismail, Mamba, Jigawa

Dr. Abubakar Saidu, Mamba, Gombe; Engr. Ahmad Y. M. Jumba, Mamba, Bauchi; Amir Abdullahi Abubakar Lamido, Mamba, Gombe.

Kazalika akwai Dr. Ibrahim Adam Omar Disina, Mamba, Bauchi; Prof. Ahmad Murtala, Mamba, Kano; Prof. Usman M. Shuaibu Zunnurain, Mamba, Katsina; Malam Ibrahim Ado-Kurawa, Mamba, Kano da Engr. Basheer Adamu Aliyu, Sakatare, Kano.

LEADERSHIP

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here