Gawa ta yi batan dabo ana shirin jana’izarta

0
185

Bacewar gawar wata dattijuwa mai shekara 63 a yayin da ake shirin gudanar da jana’izarta a ranar Asabar ya haifar da rudani a Jihar Ondo.

Gawar Misis Olajumoke Julianah Ogunsuyi ta yi batan dabo ne a dakin ajiyar gawan da ke unguwar Osii da ke garin Akure inda iyalanta, inda iyalanta suka kai gawar da nufin yi mata janaz’iza ranar Asabar.

Amma da ranar Juma’a suka je mutuwaren da ke Asibitin koyarwa na jami’ar aikin likita (UNIMED) domin daukar gawar, sai aka nemi gawar sama da kasa aka rasa.

Wata majiya mai kusanci da iyalan ta ce, “bayan mun shafe awowi muna jiran masu kula da mutuware su fito da gawar Misis Ogunsuyi, abin mamaki ba a ga gawar ba.”

Wata majiyar ’yan sanda ta ce ’yan sanda sun gayyaci jami’an asibitin da masu kula da mutuwaren domin amsa tambayoyi.

Ya ce daga baya an gano an yi musayar gawar tata ce da wata wadda za a binne a garin Oba a bisa kuskure.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ondo, Funmilayo Odunlami-Omisanya, bai yi nasara ba.

Wakilin namu ya tura mata rubutaccen sako amma bai samu amsar sakon ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here