Gwamnatin sojin Nijar ta takaita dokar hana fita a kasar

0
233

Gwamnatin Sojin Nijar ta dokar takaita zirga-zirgar da ta sanya bayan ta yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.

Dage dokar takaita zirga-zirgar na zuwa ne bayan da gwamnatin sojin ta Nijar ta katse hulda da babbar makwabciyarta Najeriya da kuma Amurka da Togo. Uwa uba, gwamnatin ta yanke hulda da tsohuwar uwargijiyar kasarsu, Faransa, sannan ta toshe kafofin yada labaran Faransar na Rfi da France24.

“Daga yau an dage dokar da takaita zirga-zirga da aka sanya ranar 26 ga watan Yuli, 2023,” in ji sanarwar da jagoran juyin mulkin kuma shugaban sabuwar gwamnatin sojin, Janar Abdourahamane Tiani, ya sanya wa hannu.

A ranar Alhamis din kuma gwamnatin sojojin ta ki ganawa da wakilan kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (ECOWAS) da Najeriya ke jagoranta.

ECOWAS ta tura wakilan karkashin tsohon shugaban kasan Najeriya na mulki soji, Janar Abdulsalami Abubakar ne domin tattaunawa da kuma mika bukatun kungiyar ga masu juyin mulkin.

A ranar ce kuma hambararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum ya aike da wasika ga Amurka da sauran kasashen duniya daga inda sojojin ke tsare da shi yana nema a dawo da shi kan mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here