Rasha ta gargadi kasashen yamma kan juyin mulkin Nijar

0
193

Fadar Kremlin ta ce duk wani yunƙurin shiga batun juyin mulkin Nijar daga ƙasashen da ba na ECOWAS ba zai ƙara lalata lamarin.

Kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov ne ya faɗi hakan sa’ilin da yake tsokaci kan kiran da hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya yi, na neman Amurka da sauran ƙasashen duniya su ɗauki matakin dawo da mulkin farar hula a ƙasar. 

Ya ce “Babu wata alama cewa shigar ƙasashen da ba na Afrika ba za su iya kawo mafita kan halin da ake ciki.” 

Ya ƙara da cewa “Muna sanya ido kan abubuwan da ke faruwa, kuma mun damu da halin tsoron da ake ciki a Nijar, muna kuma goyon bayan duk wani mataki na samar da zaman lafiya da tsaron jama’a a ƙasar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here