Kungiyoyin kwadago sun gana da Tinubu bayan gama zanga-zanga

0
154

Shugabannin ƙungiyar ƙwadago a Najeriya sun kammala ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja. 

An yi ganawar ‘yan sa’o’i bayan mambobin ƙungiyar sun yi zanga-zangar ƙasa baki ɗaya don yin tir da cire tallafin man fetur. 

Yayin zanga-zangar, ‘yan ƙwadagon sun shiga zauren Majalisar Dattawan Najeriya, inda Mai Tsawatarwa na Majalisa Sanata Ali Ndume ya tarɓe su. 

Zuwa yanzu ba a bayyana abin da ɓangarorin suka tattauna ba, da kuma ko sun cimma wata matsaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here