Sojojin Nijar sun kama manyan jami’an gwamnatin Bazoum

0
182

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun kama wasu manyan jami’an gwamnati da kuma shugaban jam’iyyar Shugaba Mohamed Bazoum.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato Jam’iyyar PNDS na sanar da kama jami’an nata a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da matsa wa sojoji lamba su koma bariki.

PNDS ta ce sojojin sun kama shugabanta Foumakoye Gado, tare da wasu ministoci na gwamnatin Bazoum.

Wadanda aka kama sun hada da Ministan Man Fetur, Mahamane Sani Mahamadou, wanda da ne na tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou.

Kazalika na kama Ministar Ma’adanai Ousseini Hadizatou.

Hakan na faruwa ne a yayin da sojojin suka zargi Faransa da kokarin yin “amfani da karfin soji” domin sake mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan kujerarsa.

Sun yi zargin ne ranar Litinin a wani jawabi da suka yi a gidan talabijin na kasar.

“A kokarinta na yin amfani da kowacce hanya da ta hada da karfin soji a kan Jamhuriyar Nijar, Faransa ta hada baki da wasu ‘yan Nijar inda suka yi taro da shugaban Zaratan Sojin Nijar domin samun amincewa a siyasance da kuma ta fuskar soji,” in ji sanarar da suka fitar.

Da ma dai ranar Lahadi Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sha alwashin daukar mataki “nan take kuma mai kaushi” idan aka kai hari kan ‘yan kasarsa a yayin da dubban masu zanga-zanga suka taru a wajen ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai.

A ranar Litinin ne ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta musanta zargin cewar ta yi amfani da mataki mai kisa majen mayar da martani kan magoya bayan sojojin da suka afka wa ofishin jakadancin Faransa a Niamey ranar Lahadi.

“Wasu mutanen da aka shirya sun kai hari kan ofishin jakadancin Faransa a Niamey jiya, lamarin da jami’an tsaron Nijar ba su dakile gabadaya ba, ” in ji sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Faransa da kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato.

“Sabanin ababen da wasu jami’an sojin Nijar ke cewa, jami’an tsaron Faransa ba su yi amfani wani mataki mai kisa ba ,” a cewar ma’aikatar harkokin wajen na Faransa.

A makon jiya ne Janar Abdourahamane Tchiani ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban Nijar kwanaki kadan bayan sojojin su yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki.

A jawabin da ya yi a lokaci, ya gargadi kasashen duniya da kada su kuskura su tsoma baki kan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar idan ba haka ba komai zai iya faruwa.

Kasashe da manyan kungiyoyin duniya sun yi Allah wadai da juyin mulkin sannan suka sha alwashin kin amincewa da sojojin na Nijar.

Kungiyar kasashen raya tattalin arizikin Afirka ta Yamma ECOWAS ta bai wa sojojin wa’adin kwana bakwai su mayar da Bazoum kan mulki ko kuma ta dauki matakin soji a kansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here