Gwamnatin sojin Nijar ta gargadi ECOWAS

0
144

Gwamnatin Sojin Nijar ta gargadi Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS a kan kada ta kuskura ta tura dakaru Jamhuriyar Nijar.

Janar Abdourahmane Tchiani wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaba yayin da zababben shugaban kasar, Mohamed Bazoum ke hannun sojoji tun bayan juyin mulkin da aka yi a makon jiya, shi ne ya bayyana hakan a wannan Lahadin.

Wannan gargadi dai na zuwa ne bayan da ECOWAS ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa’adin kwana bakwai su mayar da hambararren shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

Wannan dai shi ne matakin da kungiyar ta dauka a taron da ta gudanar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin Najeriya.

ECOWAS ta yi kira ga hukumomin sojin na Nijar da su gaggauta sakin shugaba Bazoum, tare da mayar da mulki hannun farar hula a kasar.

A sanarwar da babban jami’inta Omar Touray ta fitar, kungiyar ta ce ta yi watsi da takardar ajiye aiki da aka yi ikirarin cewa daga shugaba Bazoum take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here