Kansilolin APC sun goyi bayan nada Ganduje shugaban APC na kasa

0
190
Ganduje
Ganduje

Kansilolin jam’iyyar APC a karƙashin kungiyarsu ta NPCF su  amince da nadin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.

Kansilolin bisa jagorancin Hon Muslihu Yusuf Ali, sun bayyana haka ne cikin sanarwar manema labarai da suka fitar mai ɗauke da sa hannnun Sakataren Ƙungiyar na Ƙasa, Hon Abayomi A. Kazeem a ranar Asabar.

Kansilolin sun ce bai wa Ganduje shugabancin jam’iyyar ya yi daidai kasancewarsa gogaggen ɗan siyasa, ƙwararre wanda ya samar da ɗimbin ci gaba a Jihar Kano a zamanin gwamnatinsa.

Ƙungiyar kansilolin ta nuna godiyarta ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu dangane da zaba wa jam’iyyarsu ta APC mutumin ƙwarai a matsayin jagora.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here