’Yan ta’adda sun sace mutum 33 a Zamfara

0
126

’Yan bindiga sun sace mata akalla 23 a wani daji da kuma wasu ma’aikatan wani kamfanin gine-gine a Jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce an yi abin gaba da matan ne a wani daji da ke kusa da garin Damaga a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

Matan da suka hada da ’yan mata sun shiga cikin dajin ne domin dibar itacen girki yayin da gungun ’yan bindigar da ke kan babura suka yi awon gaba da su.

An yi garkuwa da su ne kwanaki biyu bayan kashe sojoji bakwai da wasu manoma 22 a wani artabu tsakanin sojoji da wasu ’yan bindiga a kusa da kauyen Kangon Garucci da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar.

Wani mazaunin garin, Ayuba Damaga ya ce “Mun gano cewa matanmu 23 na tare da ’yan bindigar, amma har yanzu ba su tuntubi iyalai don neman kudin fansa ba.”

A wani lamari makamancin haka, akalla ma’aikatan gine-gine 10 ne aka yi garkuwa da su a gidajensu da ke Karamar Hukumar Talata Mafara.

“Masu dauke da makamai sun mamaye gidajen mutane da misalin karfe 12:00 na daren Laraba, inda suka yi awon gaba da ma’aikatan wani kamfanin gine-gine mai suna Triacta, daga bisani kuma suka yi musayar harbe-harbe da jami’an tsaro,” in ji Aliyu Mafara.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Yazid Abubakar, ya ce ba shi da cikakken bayani game da lamarin.

“Muna bincike game da lamarin, a ba ni dan lokaci,” in ji Kakakin ’yan sandan.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here