DSS ta sake kama Godwin Emefiele bayan bada belin sa

0
180

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta sake kama Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) bayan kotu ta bada belin sa akan kudi Naira miliyan 20.

Jami’an DSS sun sake kama Emefiele ne bayan sun yi artabu da jami’an hukumar gidan gyaran hali ta Najeriya.

Fadan ya faru ne a gaban kotun Nicholas Oweibo a babbar kotun tarayya da ke Ikoyi, Legas.

Jim kadan bayan fafatawar ne jami’an gidan yarin suka fice daga harabar babbar kotun tarayya da ke Ikoyi a Legas.

Kana daga bisani jami’an DSS suka kara tisa keyar Emefiele izuwa komar su don cigaba da bincikar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here