Kotu ta bada belin Emefiele akan kudi Naira miliyan 20

0
190

Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele a kan kudi naira miliyan 20.

Sharadin belin ya hada da gabatar da wanda zai tsaya masa wanda ke da hurumi da kotun da ke Ikoyi a Legas, tare da ajiye fasfo dinsa da kuma samar da ma’aikacin gwamnati da bai gaza mataki na 16 ba don cikakken beli.

An gurfanar da Emefiele a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo da ke zama a babbar kotun tarayya da ke Legas a ranar Talata.

Masu gabatar da kara sun zargi Emefiele da samun bindigar ganga guda (JOJEFF MAGNUM 8371) ba bisa ka’ida ba.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da shi a gaban kotu cikin tsauraran matakan tsaro.

An kuma tuhume shi da laifin mallakar bindigogi da alburusai ba bisa ka’ida ba.

A cewar gwamnati, laifin ya saba wa Sashe na 4 na Dokar Makamashi, Dokokin Cap F28 na Tarayya 2004, kuma an hukunta shi a karkashin Sashe na 27 (1b) na wannan Dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here